Accessibility links

Jam'iyun Hamayya Sun Kulla Kawance a Nijar

  • Grace Alheri Abdu

Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou,

Wadansu jam’iyyun hamayya 19 cikinsu har da uku mafiya karfi a kasar suka kulla kawancen gwagwarmayar kwatar mulki a jamhuriyar

A yau ne wadansu jam’iyyun hamayya 19 cikinsu har da uku mafiya karfi a kasar suka kulla kawancen gwagwarmayar kwatar mulki a jamhuriyar. Wannan kawancen yazo ne ‘yan watanni bayan tsunduma da kasar tayi a cikin rudanin siyasa
.
Burin da wannan kawancen yake neman cimma shine na abinda suka kira tsamo jamhuriyar daga cikin halin da gwamnatin da jamhuriya ta bakwai suka saka ta a ciki. Tare da kwato al’ummar ta jamhuriyar Nijar ta hanyar shirya gwaggwarmayar kwato iko ko kuma tankwaso da mahukumtan Nijar din da su dawo daga rakiyar korar fara a daji da suka ce gwamnatin Nijar tana yi yau sama da shekaru biyu da rabi.

Dama dai an jima ana harsashen kulla kawance a tsakanin jam’iyu mafiya karfi a jamhuriyar Nijar tun ranar da jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki a jamhuriyar tayiwa wadansu ‘ya’yan jam’iyun dauk daidai kuma ta sakasu cikin gwamnatin hadin kan kasa da shugaban kasar Issouf Mahammadu ya nada a cikin watan Agustan da ya gabata.

Ga cikakken rahoton da Wakilin Sashen Hausa Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko mana.

XS
SM
MD
LG