Accessibility links

Jihar Kano Da Nijar Sun Tsaida Yarjejeniyar Ilimantarwa

  • Grace Alheri Abdu

Wadansu 'yan makaranta

An gudanar da bikin kaddamar da rukunin farko na daluban makarantar sakandaren koyon faransanci da turanci wadda gwamnatin Kano jihar tare da hadin gwamnatin Jamhuriyar Nijar suka gina a birnin Niamey

An gudanar da bikin kaddamar da rukunin farko na daluban makarantar sakandaren koyon faransanci da turanci wadda gwamnatin Kano jihar tare da hadin gwamnatin Jamhuriyar Nijar suka gina a birnin Niamey.

A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari, gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso yace gwamnatin jihar da Jamhuriyar Nijar sun yi yarjejeniya a rubuce da ta bayyana abinda kowanne bangare zai yi.

Bisa ga cewarshi, za a rika daukar yara dari-dari daga kowanne bangare a shekara. Yace yara daga jihar Kano zasu tafi Nijar su fara koyon faransanci kafin a bude makaranta sun fara iyawa da yake kananan yara ne.

Ministar ilimi ta jamhuriyar Nijar Madam Maryamu Ibrahim wadda ta wakilci shugaban kasar Mahammadu Issouf a wajen bukin da aka yi gidan gwamnatin Kano ta bayyana cewa, wannan shirin ilimantarwar zai kara dankon zumunci tsakanin kasashen da kuma fahimtar juna tsakanin ‘yan makaranta.

XS
SM
MD
LG