Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyun Siyasar Congo Sun Amince Kabila Ya Sauka a Karshen 2017


Taron da jami'iyun siyasar kasa Jamhuriyar Dimokradiyar Congo suka yi

Jami’yun siyasa a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo sun cimma wata matsaya a karshen makon da ya gabata, wacce ta nemi shugaba Joseph Kabila ya sauka daga mulki a karshen 2017.

"Al’umarmu ta na bukatar a yi zabe, mutanenmu suna bukatar canji, saboda haka yanzu mun dauki wannan hanya da za ta bamu damar cimma burinmu.” In ji Jean Marc na jam’iyar adawa ta UDPS.

Wannan matsaya da aka cimma ta samu jagorancin limamin Katolika ne, da zimmar kawo karshen rikicin siyasar kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, kana aka tsare wasu daruruwa.

A ranar 19 ga watan disambar bara Kabila ya kamata ya sauka a mulki, amma kuma aka dakatar da zaben kasar.

Hakan kuma ya sa aka yi ta zarginshi da jinkirta gudanar da zaben da nufin tsawaita wa’adinsa.

Shugaba Kabila ya fara mulkar kasar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo bayan da aka kashe mahaifinsa a shekarar 2001.

Ya kuma lashe zabe a shekarar 2006 da kuma 2011 a zabukan da ‘yan adawa suka ce an tafka magudi,.

Kundin tsarin mulkin kasar ya haramta mai sake tsayawa takara a wa’adi na uku.

Ita dai kasar ta Congo ba ta taba samun sauyin gwamnati cikin kwanciyar hankali ba, tun bayan da ta samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG