Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar APC A Taraba Ta Ki Amsar Goron Gayyatar Gwamna Darius Dickson


APC

Jam’iyyar adawa ta APC a jihar Taraba, ta ki amsar goron gayyata da gwamnan jihar Arch Darius Dickson Ishaku ya basu na hada karfi domin gina jihar, da kuma dinke rarrabuwar kawunan al’umar da ya samo asali daga jayayya da jam’iyun biyu suka yi a baya, kan halarcin wanda ya cancanci zama kan kujerar gwamna.

Shugaban jam’iyar APC na jihar Taraba Alhaji Hassan Jika Ardo, ne ya furta haka da yake amsa tambayar ko sun amince da goron gayyatar da gwamna Darius ya aikawa abokiyar takararsa ta jam’iyyar Sanata A’isha Jummai Alhassan, bayan da kotun koli ta tabbatar masa da kujerar gwamnan.

Wani mazaunin jihar Alhaji Adamu Idi ya ce rashin hadin kai sakanin jam’iyyun biyu na iya jefa matasa da ke tasowa daga baya cikin wahala da kuma koma baya ta fanni ayukan rayuwa ga jihar.

Yayin da Alhaji Maina Abdulmumini ya ce a ganinsa yana da wuya gwamnan ya samu dammar warware matsalar rikicin siyasar jihar Taraba, saboda a cewarsa goron gayyatar ta bar hanunsa amma bata isa ga ‘yan adawa ba.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

XS
SM
MD
LG