Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ce Prince Abubakar Audu Ya Rasu. Amma APC Ta Kama Hanyaar Cin Zaben Gwamnan jahar Kogi


Alamar Hukumar Zaben Najeriya INEC

Majiyoyi da dama na nuna cewa dan takarar gwamnan jahar Kogi na jam'iyyar APC ya rasu. Amma jam'iyyarsa ta APC ta sha gaba a tasoshin zabe da dama a Kogi.

Yayin da kafofi da dama ke tabbatar da mutuwar dan takarar gwamnan jahar Kogi na jam'iyyar APC, Prince Abubakar Audu, ya kama hanyar cin zaben gwamnan jahar ta Kogi, inda ya ke kan gaba a kuri’un da aka kada a wurare da dama. Kodayake akwai kuma kuri’un da aka yi watsi da su a wasu wuraren saboda dalilai dabandan.

A yanzu ana gab da kammala kirgawa. Kwamishinan Hukumar Zaben Jahar Kogi Alhaji Husaini Halilu Fai ya ce tsarin sanar da sakamakon wannan zaben ya saba da na baya. Y ace wannan karon an aba da sakamako daga runfar zabe sai a tura zuwa hedikwatar hukumar ba tare da bata lokaci ba.

Wakilan jam’iyyu dabandaban sun bayyana gwamsuwarsu game da yadda ake gudanar da zaben. To saidai tunda farko mai magana da yawun gwamna Idris Wada na jam’iyyar PDP Mr. Franc Shu’aibu ya zargi APC da shirya magudi ta wajen jibge jami’an tsaro. A yau ake sa ran samun sakamakon.

Ga wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG