Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasikun Ra’yin Masu sauraren Sashen Hausa na Muryar Amurka VOA


Wata motar a kori kura ce nan dauke da hotunan gangamin zaben shugaban Nigeria Goodluck Jonathan a birnin Ikkon Nigeria.

Zaben 2011 na Najeriya

Wasikar farko a yau Alhamis 13/04/2011 ta fito ne daga Malam Buba Mai Goro da Malam Zubairu Gashuwa Gashua dake cewa jam’iyyun adawar Nigeria kamar su CPC da ANC, da ANPP dasauransu, a zahiri kun bar Jaki ne kuna dukan Taiki domin sakacin ku da kwadayin son mulkin ku, zai janyowa faduwarku a zabe. Goodluck Jonathan zai sami nasarar zabe a banza, ya kamata ku sake lale ku gaggauta yin shawara mai karfi daga nan zuwa Juma’a kumarawa mutum daya baya domin har yanzu da sauran lokaci.

Shi kuwa Malam Aminu Abdu Bakanoma Sani Mai-Nagge Kano Nigeria ya aiko da wasikar dake cewa Assalamu alaikum. Ina kira gajam’iyyun adawa musamman CPC da CAN ya kamata kowayaajiye bukatunsa ku sasanta. Domin sasantawarce kadai hanyar da za’a iya samun nasara da hadin kai, hadin kan shine samun nasarar a zaben nan mai zuwa. 13/04/2011.

Shi kuma Komred Muhammad Khalil Marmarqa jihar Katsinan Nigeria ya aiko da wasikar dake cewa, Talakan Nigeria bawan, Allah, wai a yau a Nigeria talauchi da mutuwar zuciyar talaka tasa har zai iya saida ‘yancinsa da na iyalinsa har tsahon shekaru hudu a kan kudi Naira metan da sabulai, kumaabintakaici har sai Talakan yarantse, haba Talakan Nigeria yanzu har kun manta da irin ukubar da muke ciki ne? 13/04/2011

Shi kuma Malam Isah Tarkunya jiharBauchin Nigeria ya aiko da wasikar dake cewa ayi hattara domin Kabilanci da addini ya dabaibaye zukatan ‘yan Nigeria, musamman ‘yan Arewaci. Allah ka kawo gyara. Shi kuma malamTukur Shehu Badariya B/Kebbi ya aiko da wasikar dake cewa Muryar Amurka ka fadawa ‘yan jam’iyyar CPC a ko ina suke tun daga kan shugabanni zuwa kan wakilai (membobin jam’iyya) musamman a jihohin da jam’iyyar PDP tayi abinda tafi kwarewa kansa wato magudin zabe a jihaohin Kebbi, Sokoto, Kano, Jigawa, bauchi, da Filato, taraba,Benue, Adamwa, Borno, Yobe. Saifa kun tashi tsaye a zaben nan mai zuwa domin kare kuri’arku domin hana afkuwar abinda ya faru a zaben ‘yan majalisar tarayya. 13/04/2011

Shi kuwa Malam Usman Taka lafiya B/Kebbi ya aiko da wasikar dake cewa Ina kira ga shugaban hukumar zaben Nigeria, Farfesa Muhammad Attahiru Jega, da ya kara saka ido kan wadansu Kwamishinonin zabe dake a wasu jihohin Nigeria harda su kansu kananan ma’aikata hukumar zaben Nigeria, doming a dukkanalamu a wadansu jihohin har yanzu bata chanza ba. 13/04/2011

Sai kuma wasikar da ta fito daga wajen Malam Sani World 7 Kusfa Zaria dake cewa Allah Sarki jama’ar Nigeria anyin walkiya munga Kura a tsugune, ya kamata ran Asabar mai zuwa sha shida ga wata mu fito kwanmu da kwarkwatar mu mu zabi Janar Muhamad Buhari don mu kubuta daga wannan kangi da muke ciki da jam’iyyar PDP ta sakasu ciki. Allah ya bada sa’a amin. 13/04/2011

XS
SM
MD
LG