Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Libertarian Ta Tsunduma Cikin Takarar Shugabancin Amurka


Gary Johnson, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Libertarian

Amurkawa sun saba da jam'iyyu biyu kodayake wani lokacin lotoloto a kan samu wani ya fito takarar shugaban kasa ko a zaman indifenda ko kuma da sunan wata jam'iyya -

Jiya wani tsohon sanata Gary Johnson wanda ba'a sanshi sosai ba ya fito tsayawa takarar shugabancin kasar Amurka a daidai lokacin da yawancin mutanen kasar ba sa son Trump na Republican ko Clinton ta Democrat.

Bin ra'ayin jama'a da aka yi jim kadan bayan ya bayyana kansa, Gary Johnson dan shekaru 63 da haihuwa, wanda kuma tsohon dan Republican ne da yayi gwamnan jihar New Mexico tsakanin shekarun 1995 da 2003 kafin ya canza sheka zuwa jam'iyyar Libertarian, ya samu goyon bayan kashi 10 cikin masu kada kuri'a a duk fadin kasar idan aka kwatantashi da Trump ko Clinton,

Haka ma taron kolin da jam'iyyar tayi a Orlando dake jihar Florida an zabi William Weld ya zama mataimakin Gary Johnson. Shi dai Weld ya taba zama gwamnan jihar Massachusetts.

Idan aka bi tarihin 'yan takara na uku a zaben shugaban kasa bai taba yin tasiri ba a zabukan baya. Sau tari ma sukan shude da zara an kusa da zaben shugaban kasa. A wannan karon idan har Gary Johnson ya cigaba da samun kashi 10 kacal da wuya ya kai labari gida a kowace jiha cikin jihohi 50.

To saidai idan an bi sakamakon zaben jiha jiha yana iya shafar sakamakon zaben musamman idan aka yi la'akari da cewa kusan kashi 50 na masu jefa kuri'a a duk fadin kasar suka ce ba sa son Trump ko Clinton. Kuma a zaben shugaban kasar Amurka ba yawan kuri'u ke ba dan takara nasara ba, a'a nasarar jiha zuwa jiha ce kuma jihohin da suka fi yawan kuri'u su ne suka fi mahimmanci.

XS
SM
MD
LG