Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani jirgin Saman Soja Na Kasar Myanmar Ya Bace


Mafi yawancin fasinjojin Iyalan sojojin Kasar ne.

Wani jirgin saman soji na kasar Myanmar dake dauke da mutane sama da 100 ya ba ta, yayin da ya tashi daga kudancin kasar zuwa yankin Yangon, in ji hukumomin kasar ta Myanmar a yau Laraba.
Rahotanni sun ce mafi yawan fasinjojin iyalan sojojin kasar ne, wadanda suka taso daga birnin Myeik da ake kira Mergui a kudu maso gabashin kasar ta Myanmar.
Kuma tafiya daga wadanda yankuna ya hada har da ketara tekun Andaman.
Wani jami’in kasar ya fadawa Muryar Amurka cewa an tsinci wasu sassan jirgin a tekun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG