Accessibility links

Jam’iyyar PDP na ci gaba da bikon ‘ya’yanta


Tambarin jam'iyyar PDP

Wakilin Muryar Amurka a Abuja Hassan Maina Kaina ya hada manarahoton da wasu ‘yan PDP da masana siyasa ke ganin sai fa jam’iyyar APC mai mulki ta yi da gaske kar Jam’iyyar da ta fadi zabe ta PDP ta farfado daga dogon suman da ta yi.

Jam’iyyar PDP ta sami tirka-tirkar shugabancin da a karshe suka rasa karfin mulkin Najeriya da a da suke rike da ragamar jagorancin kasar. To amma wasu ‘ya’yanta sun nuna cewa har yanzu da sauran ran PDP don kuwa suman da tayi tana iya farfadowa matukar jam’iyyar APC ta yi sakaci, don ba mutuwa tayi ba kamar yadda wasu ke zato.

Barista Abdullahi Jalo yana tabbatar da cewa har yanzu jam’iyyar PDP na ci gaba da bikon ‘ya’yanta da suka yi fushi suka koma jam’iyyar APC mai mulki a yanzu da it ace ta rangada PDP din da kasa. Solomon Dalung na daya daga cikin kusoshin APC yace duk sumbatu ‘yan PDP ke yi kawai.

Shi kuwa Buhari Bello Jega kuwa masani kan kimiyyar siyasa a Jami’ar Abuja cewa yayi, in dai jam’iyyar APC ta tsaya kunbiya-kunbiya toi suna ji suna gani PDP za ta dawo da karfinta daga dogon suman da ita yi don har yanzu da sauran numfashinta.

XS
SM
MD
LG