Accessibility links

Mutane Suna Kauracewa Jihohin Da Aka Kafa Dokar-Ta-Baci

  • Grace Alheri Abdu

Wata Mace da 'ya'ayanta da suke kokarin kauracewa Maiduguri

Mazauna jihohin da aka kafa dokar-ta-baci suna kauracewa jihohin sakamakon rashin abinci da kuma zaman fargaba.

Jama’a da dama na ci gaba da kauracewa jihohin da aka kafa dokar-ta-baci zuwa wadansu jihohi da kuma kashe dake makwabta.

Rahotanni na nuni da cewa, mutanen da suke tafiya gudun hijira sun bayyana cewa, ya zama dole su kauracewa matsugunansu domin rashin kayan masarufi da muhimman ababan jin dadin rayuwa.

Sun kuma bayyana cewa, banda yunwa, suna zaune a cikin tashin hankali. Wadansu daga cikin ‘yan gudun hijiran da suka isa Gombe daga Maiduguri da wakilinmu Abdulwahab Mohammed ya yi hira da su sun bayyana irin halin da suka shiga kafin suka isa garin Gombe.

XS
SM
MD
LG