Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyun Adawan Zimbabwe Na Shakkan Za'a Yi Zabe Cikin Lumana


Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa na jam'iyyar ZANU-PF,
Shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa na jam'iyyar ZANU-PF,

Rashin kasancewar wakilin jam'iyyar dake mulki wurin kaddamar da kundun kare hakkin bil Adama ya sa jam'iyyun adawar kasar shakkan ko za'a gudanar da zaben kasar cikin lumana

Jam’iyyyun adawa a Zimbabwe sun fara nuna shakkun cewa jam’iyya mai mulki ta ZANU-PF, ba za ta gudanar da zabe cikin Lumana ba nan gaba a wannan watan.

Wannan kokwanto na zuwa ne, bayan da aka gaza samun halartar ko daya daga cikin wakilan jam’iyyar wajen bikin kaddamar da wani kundin manufofin kare hakkin bil Adama da kungiyar Amnesty International ta jagoranta a jiya Alhamis.

Da yawa daga cikin mambobin sauran jam’iyyun siyasar kasar sun halarci taron a lokacin da kungiyar ta Amnesty International ta kaddamar da manufofin kare hakkin dan adam a Harare, babban birnin kasar.

Mataimakin shugaban kungiyar a kudancin Afirka, Muleya Mwananyanda, ya ce kasar ta Zimbabwe ta fuskanci matsalolin take hakkin bil Adama a shekarun baya, kamar na tilsatawa mutane su bace a kasar.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama da dama, sun sha zargin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe da yin amfani da tsare jama’a da azabtarwa da yin garkuwa da mutane domin ci gaba da zama a kan karagar mulki.

Amma mataimakin shugaban kungiyar ta Amnesty, ya ce wannan lokaci ya wuce.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG