Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyun Siyasa Dake Adawa A Nijar Sun Kafa Sabon Kawance


Taron jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da suka kafa sabon kawance
Taron jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula da suka kafa sabon kawance

Gamayyar jam’iyyun siyasa dake adawa da wasu manufofin gwamnati sun kafa sabon kawance da kungiyoyin fararen hula da zummar matsawa gwamnati ta soke dokar karin haraji dake cikin kasafin kudin shekarar 2018

Jam’iyyun hamayya na jamhuriyar Nijar sun bada sanarwa kafa wani sabon kawancen adawa da gwamnatin kasar.

Kawancen na FDR ya kunshi jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula a ci gaba da nemo hanyoyin ceto Dimokradiya a kasar ta Nijar daga barazanar da take fuskanta.

Malam Aminu Isiya kusa ne a jam’iyyar MODEN Lumana, jam’iyyar dake kan gaba a wannan sabon kawancen adawan. Yace yaki irin wannan kawance, bai yiwuwa sai da hadin kai. Dalili ke nan suka hada kai suka yi kawance domin su ceto kasar tare da ceton talakawa.

A cewar Isiya kawancen ba wani abu sabo ba ne domin sun taba yin hakan lokacin da Tanja Manmadou ya yi kokarin yin tazarce. A wancan lokacin shugaban kasa na yanzu yana cikin kawance.

Kungiyoyin fararen hula dake adawa da dokar harajin shekarar 2018 kwana kwanan nan suka matsawa gwamnati lamba da ta soke wasu sabbin harajin da suka yi zargi ta haddasa tsadar rayuwa. Suna ganin wannan sabuwar kawance tamkar faduwa ce ta zo daidai da zama.

Gamaje Muhammadou na kungiyar Sinkotasi. Ya ce ya kamata duk su tashi su ceto ‘yancin kasarsu daga gwamnatin kasar. Ya ce kowa ya san yanzu babu Dimokradiya.

Sai dai a martanin da hadiman shugaban kasa suka fitar sun ce babu kawancen da zata iya fitar dasu daga mulki saboda yadda talakawa ke nuna gamsuwa da ayyukan ci gaba da gwamnati ke yi masu.

Sluley Barma na da karin bayani a rahotonsa

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG