Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Buhari Yace Yananan Daram a APC


Buhari da Tinubu
Buhari da Tinubu

Daya daga cikin jiga jigan jam'iyyar APC mai hamayya a Najeriya Janar Mohammadu Buhari mai ritaya ya karyata jita-jitar cewa zai bar jam'iyyar zuwa jam'iyyar Labor.

Daya daga cikin shugabannin babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya APC janar Muhammdu Buhari mai ritaya, ya zargi jam'iyyar PDP da kasancewa kanwa uwar gamin yada jita jitar cewa zai fice daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar Labor, saboda "wai" da akwai rashin jituwa tsakaninsa da wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar.

Janar Buhari wanda ya musanta wannan jita-jitar a hira da yayi da Sashen Hausa na Muriyar Amurka, yace zancen canza jam'iyya bata ma taso ba saboda babu daili, domin shi ba da ka haka yake tafiyar da al'amari ba, mataki da ya kai ga kafa ita jam'iyyar APC.

Janar Buhari yace PDP wacce take da jihohi fiyeda ashirin da kuma tarayya ta kasa kimtsa kanta, saboda haka take neman amfani da jita jita domin ta gwadawa duniya cewa APC wacce take take kimtsatstsiya ce tana da matsaloli tsakaninta. Janar Buhari yace ya hakikance PDP ce sarsalar wannan jita-jita, idan ba haka wa zai fito da maganar cewa zai koma jam'iyyar Labor, maganar da bata da tushe

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG