Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jaririyar da Aka Haifeta Zuciyar ta a Waje ta Rayu


Jaririya a Birtaniya
Jaririya a Birtaniya

Jami’an asibitin Birtaniya sun ce jaririyar da aka Haifa zuciyarta na waje ta rayu, bayan an samu nasarar tiyata da ak yi mata sau uku.

Asibitin Glenfield dake birin Leicester ya fada a jiya Laraba cewar jaririya mai suna Vanellope Hope Wilkins da aka haifa a karshen watan Nuwamba, zuciyarta na girma ne a wajen jikinta, wani lamari na ba saban ba.

An yi mata tiyata na farko inda aka mayar da zuciyarta a cikin jikinta bayan awa daya da haifuwarta.

Dr. Nick Moore yace jaririyar tana kwance a sashen kula na musamman da aka kebe na jarirai.

Jarirai takwas kadai a cikin kowadanne jarirai miliyon ne ake haifa da zuciya a wajen jikinsu. Kuma galibin wadanda ake haifuwa da wannan matsala ne suke mutuwa cikin kwanaki uku da haifuwar su.

Likitoci masana aikin zuciya sun ce basu da masaniya a kan wani jaririn dake fama da wannan matsala ya rayu ko ya samu lafiya bayan tiyata a kasar Britanniya. Amma jarirai masu wannan matsala da dama sun rayu a Amurka bayan an yi musu tiyata ciki har da Audrina Cardenas wacce aka haifa a jihar Texas a shekarar 2012.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG