Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jerin Sunayen Sabbin Ministoci A Najeriya Da Shugaba Buhari Ya Zaba


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Ibrahim Lawan ya karanta wasikar da Shugaba Muhammadu Buhari, ya aika wa Majalisar dauke da sunayen Ministoci da yake so, a tantance mutum 43, wanda a ciki an samu tsofaffin Ministocin sa 10 wadanda suka yi aiki da shi a wa'adin sa na farko.

Akwai tsohon Ministan Kimiya Ogbonanya Onu, Chris Nigige, Geofrey Onyeama, Rotimi Chibuike Amechi, Osagie Ehanire, Babatunde Raji Fashola, sai Abubakar Malami, Adamu Adamu, Zainab Shamsunah Ahmed, da kuma tsohon Ministan watsa labarai Lai Mohammed.

Acikin sababbi akwai fitattu irin su Sheik Isa Ibrahim Aliyu Fantami, Sanata George Akume wanda ya taba zama gwamnan jihar Benuwai, da Sanata Godwill Akpabio wanda shi ma ya taba zama gwamnan jihar Akwa Ibom, sai tsohon gwamnan jihar Bayelsa Timipre Sylva, kana da tsohuwar shugabar Mata ta Jamiyar APC Dr. Ramatu Tijjani.

Mai fashin baki a al'amuran yau da kullun Mohammed Ishaq ya ce shugaba Buhari, ya maido da tsofaffin ministocin ne saboda sun shaku da shi, kuma sun saba aiki da shi, kuma yana ganin cewa suna da alkibla daya.

Don kawo wa kasa irin canjin da shugaba Muhammadu Buhari ke ikirari tun lokacin da yake yakin neman zabe kafin wa'adinsa na farko a shekara 2015, sabo da haka abinda 'yan kasa ke jira shi ne su ga irin wannan canji a rayuwar su ta yau da kullun.

A yanzu dai babu tabbacin ko majalisar zata tantance ministocin kafin lokacin hutun ta na wattani biyu, wanda ya kamata ta fara shi a ranar Alhamis 25 ga wannan wata.

Ga cikakken rahoto daga wakiliyar muryar Amurka Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG