Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Xi Jinping Ya Isa Hong Kong


Shugaban kasar China Xi Jingping
Shugaban kasar China Xi Jingping

Shugaban China Xi Jingping na kan wata ziyara a birnin Hong Kong a wani mataki na halarta bikin cikar yankin shekaru 20 bayan mulkin mallaka da Birtaniya ta ma yankin.

Shugaban kasar China Xi Jinping ya fara ziyarar kwanaki uku a birnin Hong Kong yau Alhamis don bikin cika shekaru 20 tun bayan da kasar Burtaniya da ta mulki kasar ta maida kasar a hannun hukumomin kasar ta China.

Haka kuma a lokacin wannan ziyarar, Mr. Xi zai halarci bukin rantsa rda Carrie Lam, wadda ita ce mace ta farko da za a rantsar a matsayin shugabar kasa a Hong Kong a ranar Asabar.

An tsaurara matakan tsaro a fadin birnin kuma ‘yan sanda sun kama wasu masu zanga-zangar nuna goyon bayan dimokradiyya gabanin isar Mr. Xi.

Ana sa ran ganin tarukan zanga-zanga, ciki har da jerin gwanon da aka saba yi duk shekara ranar Asabar, wanda a baya yake janyo gangamin dumbin jama’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG