Accessibility links

Jihar Nassarawa ta Najeriya ce ta bakwai a jerin jihohin da aka fi fama da cutar kanjamau


Masu ilimin kimiyya suna ci gaba da neman maganin cutar kanjamau

Rahoton yaki da cutar kanjamau na baya bayan nan a Najeriya na nuni da cewa, jihar Nassarawa ce ta bakwai a jihohin da aka fi samun masu fama da cutar ko kuma wandada suke dauke da kwayar cutar HIV.

Rahoton yaki da cutar kanjamau na baya bayan nan a Najeriya na nuni da cewa, jihar Nassarawa ce ta bakwai a jihohin da aka fi samun masu fama da cutar ko kuma wandada suke dauke da kwayar cutar HIV.

Jami’in gudanar da ayyukan yaki da cutar kanjamau na jihar Ibrahim Azara ne ya bada bayyana haka a Lafiya fadar mulkin jihar Nassarawa.

Barista Azara ya bayyana cewa cibiyar yaki da cutar kan jamau ta jihar Nassarawa tana fuskantar gagarumar kalubala da zata iya gurguntar da yunkurin shawo kan cutar, bisa ga cewarshi, wannan na iya haddasa ci gaba da yada cutar ya kuma haifar da koma bayan tattalin arziki.

Barista Azara yace matsalolin da cibiyar yaki da cutar kanjamau ta jihar Nassarawa ke fuskanta sun hada da karancin ma’aikata, da kwararru a fannin yaki da cutar kanjamau, da rashin ofisoshi. Sauran matsalolin kuma sun hada da karancin kudi da kayan aiki.

Barista Azara ya yi kira ga gwamnatin jihar Nassarawa da ta maida hankali wajen aiwatar da tsare-tsaren da zasu tunkari wadannan kalubalai domin a iya shawo kan cutar.

Barista Ibrahim Azara ya bayyana haka ne yayin kaddamar da shirin yaki da cutar kanjamau na Bankin Duniya da ake kira “Multi-Country HIV/AIDS Programme (MAP).

Bankin Duniya ya kirkiro da wannan shirin ne a shekara ta dubu da dari tara da casa’in da tara a matsayin shiri mafi girma na yaki da cutar kanjamau. Ya kuma kebe dala miliyan dubu dari biyu domin yaki da cutar kanjamau karkashin wannan shirin, wanda za a gudanar a kasashen talatin da biyar na duniya, da ya hada da ayyukan da za a gudanar a yankuna shida na duniya, inda za a maida hankali kan matsalolin da suka addabi kasashen yankunan.

Bankin Duniya ya kaddamar da wannan shirin karon farko a Afrika cikin shekara ta dubu biyu. Za a a gudanar da shirin ne cikin shekaru goma sha biyar, a matakai uku.

Babban Bankin Duniyan zai gudanar da shirin ne tare da hadin guiwar gwamnatoci, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma al’umma.

Manufar shirin Yaki da cutar kanjamau na Bankin Duniya (MAP) shine samar da magunguna da kulawa da kuma jinyar masu dauke da kwayar cutar, musamman tsakanin marasa karfi kamar matasa da matan da shekarunsu basu wuce haihuwa ba, da mata masu zaman kansu da kuma ‘yan luwadi da madigo.

Jihar Nassarawa na daga cikin jihohin da aka kaddamar da wannan shirin a Najeriya.

XS
SM
MD
LG