Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JIHAR NEJA: PDP Ta Nuna Damuwa Kan 'Yan Fashin Daji Da Ke Ci Gaba Da Kisan Jama’a


Zauren taron jam'iyyar PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Nejan Nigeria ta nuna damuwa matuka akan yadda ‘yan fashin daji ke ci gaba da hallaka jama’a a sassa daban daban na jihar.

PDP dai wadda a karon farko cikin ‘yan shekarun nan da matsalar rashin tsaron ta kara ta’azzara a jihar Nejan aka ji ta yi magana a wani babban taron da ta gudanar a garin Kontagora cibiyar yankin arewacin jihar Nejan, mai fama da tashin hankalin ‘yanbindiga.

Tace lamarin abin tayar da hankali ne bisa la’akari da yadda aka rufe makarantun bako a yankin jigon PDP a jihar Nejan.

A hirar ta da Muryar Amurka, Uwar gidan tsohon gwamnan jihar Sanata Zainab Kure tace akwai bukatar daukar matakin gaggawa.

A nashi bayanin, Hon. Yahaya Ability mataimakin shugaban PDP mai kula da yankin Arewacin Jihar Neja, ya ce sun je Kontagoran ne domin jaje akan matsalar ‘yan bindiga da su ka addabi yankin.

Akwai alamun PDP za ta yi amfani da matsalar rashin tsaron domin neman ma kanta farin jini a babban zaben shekara ta 2023 mai zuwa domin kuwa shugaban PDP a jihar Nejan, Barista Tanko na cewa “jami’yyar PDP a Najeriya da ma PDP na jihar Neja ne za su dawo mana da martabanmu saboda an wahala. Jiki magayi, ba haka aka so ba, amma ya zama darasi garemu.”

Gwamnatin APC dai ta ce tana daukar matakin shawo kan lamarin, inji sakataren gwamnatin jihar Nejan Ahmed Ibrahim Matane.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG