Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Texas Ta Kafa Dokar Barin Masu Lasisi Zuwa Makaranta da Bindigoginsu


Texas Gov. Greg Abbott , gwamnan jihar Texas

Hukumomin jihar Texas dake nan Amurka sun ce daga yanzu zasu rinka barin wasu masu lasisin mallakar bindigogi, ciki harda dalibbai, da zasu iya daukar bindigogin nasu har zuwa ajujuwansu na karatu a makarantunsu.

Masu goyon bayan wannan sabon tsarin da ya soma aiki daga jiya Litinin, sunce zai taimaka wajen hana yawan hare-haren da ake kaiwa makarantu, yayinda masu adawa da shirin ke cewa ba abinda zai haifar sai dada jefa ‘yan makaranta cikin hatsari.

Gwamnan jihar da wasu manyan jami'an jihar lokacin da suke tabbatar da sabuwar dokar
Gwamnan jihar da wasu manyan jami'an jihar lokacin da suke tabbatar da sabuwar dokar

Galibin ‘yanmajalisar dokokin jihar da kuma shi kansa gwamnan jihar ta Texas, Greg Abbot, duk sun goyi bayan wannan sabon shirin da yasa jihar texas ta shiga rukunin jihohin kalilan na Amurka dake da irin wannan dokar da ta baiwa mutane dama su rinka yawo da bindigoginsu.

XS
SM
MD
LG