Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Amurka: Ina Aka Dosa Bayan Manyan Taruka?


Donald Trump (Hagu) Hillary Clinton (Dama)

Bayan da aka kammala manyan turakan jam’iyyun siyasa a Amurka, yanzu hankula za su karkata ne akan ‘yan takarar da jami’yyun suka fitar, wato Donald Trump a karkashin jam’iyyar Republican da kuma Hillary Clinton a bangaren jam’iyyar Democrat.

Dukkan ‘yan takarar sun kwashe kusan shekara suna neman masu kada kuri’a su yi rijista a karkashin jam’iyyunsu, amma akwai kuma da yawa daga cikin masu kada kuri’ar da suka zabi zama a kujerar ‘yan ba ruwanmu.

Wannan nau’in masu kada kuri’a da ke saman katanga, su ne za su kasance bangaren da ‘yan takarar za su fi maida hankulansu akansu, domin neman su kada musu kuri’a a watan Nuwamba.

NEMAN KUDADEN KAMFE DA YADDA ZA A KASHE SU

Yanzu wani muhimmin batu ga Clinton da Trump shi ne yadda za su yi zawarcin masu ba da gudunmuwa domin samun kudaden yin kamfe.

“Ya na da muhimmanci, kowane bangaren masu kamfe a duk jam’iyyun su samu kudade, domin sai an ware kudaden biyan ma’aikata da ke yiwa jam’iyya hidima a juhohi daban daban, fiye da wadanda za a ware domin tallata dan takara a kafafen yada labarai.” In ji Penny Lee, kwararriya a fannin tsare-tsaren jam’iyyar Democrat, yayin wata hira da ta yi da Muryar Amurka.

Alkaluma na baya bayan nan da hukumar zaben Amurka ta fitar sun nuna cewa, kwamitin yakin neman zaben Clinton ya fara da dala miliyan 44 a asusunsa a watan Yuli idan aka kwatanta da dala miliya 20 da na Trump ya fara da shi.

Sannan Clinton ta kashe dala miliyan 230 idan aka kwatanta da dala miliyan 70 da Trump ya kashe tun da aka fara yakin neman zaben.

Tarihi ya yi nuni da cewa, wannan kashe kudade da ‘yan takarar biyu ke yi somin tabi ne, domin kwamitin yakin neman zaben shugaba Barack Obama, ya kashe dala miliyan 775 daga aljihunsa kadai kafin a sake zaben shi a shekarar 2012.

Sannan abokin hamayyarsa, Mitt Romney na jam’iyar Republican ya kashe dala miliyan 460.

Baya ga haka dukkan jam’iyyun da sauran kungiyoyi na waje sun kara kashe wasu makudan kudade a lokacin.

MUHAWARA

Kamar yadda aka gani a lokacin yakin neman zaben fidda gwani na jam’iyyun, haka ake sa ran za a ci gaba a wannan salo a nan gaba a yunkurin 'yan takarar na shiga Fadar White House, inda ‘yan takarar za su ci gaba da yin gangami a garuruwa a duk fadin kasar.

Sai dai za a fi maida hankali ne a juhohin da suke da muhimmanci a kasar, wato juhohin da akan yi kare jini biri jini, wadanda suka su fi yawan kuri’u.

Wadannan juhohi sun hada da Florida da Ohio da Pennsylvania.

Banbancin da ke tsakanin tarukan da za a yi a watannin Agusata da Satumba da kuma wadanda aka yi a watan Maris, shi ne ba za a yi zabe a karshensu ba kamar yadda aka gani a lokacin zabukan fidda gwani.

Sai dai ‘yan takarar za su yi fatan sakonnin da suka fadawa masu kada kuri’a za su zauna a zukatansu har sai watan Nuwamba a lokacin da za a kada kuri’a.

Wani muhimmin lokaci da ke tafe, shi ne na ranar 26 ga watan Satumba,a lokacin da Clinton da Trump za su kara a muhawarar farko.

Sannan su sake haduwa a muhara ta biyu a ranar 9 ga watan Oktoba da kuma haduwa ta karshe a ranar 19 ga watan Oktoba.

Baya ga haka mataimakan ‘yan takarar biyu, wato gwamnan jihar Indiana Mike Pence da Trump ya zaba da kuma Sanata Tim Kaine da Clinton ta zaba, za su yi muhawara sau daya ne tak, wato a ranar 4 ga watan Oktoba.

“Mutane za su samu damar ganin yadda su biyun za su kaya ba tare da ‘yan kallo sun sa baki ba, wanda hakan zai ba da damar a yi binciken kwakwaf kan yakin neman zaben bangarorin biyu.” Lee ta kara da cewa.

Dukkanin muhawarorin dai za a kwashe minti 90, kuma za a yada su ne kai tsaye ta kafofin talbijin. Za kuma gayawa kowane dan takarar maudu’in da za a tattauna akai, amma ba tare da an gaya masu takamaiman tambayoyin da za a masu ba.

Hakan zai ba su damar yin bita ko kuma takarar irin sukar da abokin hamayya zai iya domin su san yadda za su kare kansu.

“A baya, ba kasafai muhawara ke yin tasiri ba, saboda mafi yawan mutanen da ke kallo, mutane ne da suka riga suka san wanda za su zaba, amma ina ga wannan karo zai zama wani batu ne daban, wato abu mai nishadantarwa.” Kwararriya a fannin tsare-tsare ta jam’iyyar Republican Lisa Spies ta gayawa Muryar Amurka.

Sai dai akwai yuwuwar za a iya samun dan takarar shugaban kasa na uku daga wata jam’iyya, wanda zai iya ba da wata dama ta daban a fagen siyasar ta Amurka da jam’iyyun Republican da Democrat sukan mamaye.

Amma ka’idar shiga muhaawarar ita ce har sai dantakara ya samu shiga a juhohi da dama tare da yuwuwar zai iya lashe zabe sannan ya samu kashi 15 da ke mara mai baya a zabuka akalla guda biyar na kasa baki daya.

Yanzu haka dan takara na uku na jam’iyyar Libertarian Gary Johnson ya na yawo ne tsakanin kashi biyar zuwa 10.

RANAR KECE RAINI

Bayan an kammala tafka muhawara, kwamitin yakin neman zaben kowace jam’iyya zai ci gaba jan hankulan masu zabe, musamman wajen ganin sun fita sun kada kuri’unsu.

A zaben shugaban kasa na shekarar 2012, kusan kashi 55 ne da suka isa kada kuri’a suka fita zabe.

Ranar zabe a Amurka, ba rana ce da aka kebe a matsayin ranar hutu ba, koda ya ke akan rufe wasu makarantu a wurare da dama, domin ana amfani da su a matsayin rumfunan kada kuri’a.

Akan yi zaben ne ranar Talata, ana kuma kwashe sa’oi 12 ana zaben a kowace jiha.

Akan kuma bayyana sakamakon zaben ne ba da jimawa ba bayan an rufe rumfunan zabe, sai dai kawai idan an dakatar da zaben wani yanki.

Al’umar kasar, ta san wanda ya lashe zabe a wannan dare, amma ba za a bayyana sakamakon a hukumance ba har sai ranar 6 ga watan Janairu.

Dalili kuwa shi ne, Amurka na amfani ne da wani tsari da ake kira “Electoral College,” wato tsarin da ke ware wasu wakilai na musamman a kowace jiha bisa yawan al’umar jihar a duk fadin kasar, illa juhohi biyu.

Dan takarar da ya fi samun yawan kuri’un wadannan wakilai shi ne ya lashe zaben, wato duk wanda ya samu kuri’ar wakilai 270 daga cikin kuri’un wakilai 538 shi ne zai zama shugaban kasa.

Wannan tsari na nufin duk wanda ya fi yawan kuri’u a zaben da aka yi a duk fadin kasar ba lallai ya zama shi ya lashe zaben, kamar yadda aka gani a lokacin takarar Al Gore na jam’iyyar Democrat a shekarar 2000 bayan da ya samu yawan kuri’u a duk fadin kasar, amma kuma ya gaza samun kuri’un wakilai fiye da wanda Goerge W. Bush ya samu.

Idan har Trump da Clinton suna so su lashe zaben shugaban kasa, dukkan ‘yan takarar sai sun yi kokari sun wanke kansu daga sukar da aka masu a idon masu kada kuri’a.

“Ina ganin a bangaren Donald Trump, dole ya fara gabatar da kansa kamar shugaban kasa, ba wai ya rika garzayawa shafin Twitter ya rubuta kalmomi 140 domin nuna matsayarsa ba, tare kuma da tsayawa akan duk wata magana da ya yi. Sannan ita kuma Clinton akwai bukatar ta kara jan mutane a jika, ta saka kanta a irin halin da su ke ciki, sannan ta ci gaba da nuna cewa ita shugaba ce da za a yarda da ita. In ji Lee.

Wanda ya lashe zaben zai shiga ofishi ne a ranar 20 ga watan Janairu.

XS
SM
MD
LG