Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Yobe ta kara kason kudin yaki da cutar shan inna


Maikacin gwamnati tana ba yara maganin cutar shan inna
Maikacin gwamnati tana ba yara maganin cutar shan inna

Bayana na nuni da cewa, kananan yara sittin da biyu suka kamu da cutar shan inna a jihohi takwas na arewacin kasar Najeriya.

Bayana na nuni da cewa, kananan yara sittin da biyu suka kamu da cutar shan inna a Najeriya, yayinda kawo yanzu aka tabbatar da yara masu dauke da cutar a jihohi takwas na arewacin kasar.

A shiyar arewa maso gabas an sami bullar cutar a jihohin Yobe da Borno da Bauchi bana. Ta dalilin haka, gwamnatin jihar Yobe ta kara kudin da ta kiyasta na yaki da cutar daga naira miliyan shida zuwa miliyan goma bayan gabatar da wadansu sababbin shirye domin yaki da cutar.

Mataimakin gwamnan jihar Injiniya Abubakar Aliyu wanda kuma shine mai sa ido kan ma’aikatar lafiya ta jihar ne ya bayyana haka jim kadan bayan wani taron polio a jihar.

Mataimakin gwamnan yace za a kara kaimi wajen fadakar da iyaye wadanda suke shakkun bari a yiwa ‘ya’yansu rigakafin. Ya kuma bayyana muhimmancin ‘yan jaridu a cimma nasarar wannan yunkurin.

Injiniya Aliyu ya yi kira ga shugabanni su kara himma wajen ganin an shawo kan cutar yayinda yayi kira ga al’umma su rika bari ana yiwa ‘ya’yansu alular rigakafin yayinda kuma ya shawarce su rika tsabtace muhallinsu.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG