Accessibility links

Jihohin Borno da Yobe da Kuma Adamawa na Cigaba da Fuskantar Matsalar Tsaro


Mata na duba gidajen da harin Boko Haram ya lalata a garin Bama.

Ganin yanda alamuran tsaro ke daukan sabon salo a jihohin Borno da Yobe da Adamawa,dukansu suna cikin doka ta baci.

Ganin yanda alamuran tsaro ke daukan wata salo a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa dukansu ke cikin dokar tabaci.

Ana cigaba da fuskantar matsalar hare-hare dake haifar da hasaran rayuka da dukiyoyi masu dunbin yawa,duk da irin matakan taro da hukumomi kan dauka.

Irin wanna ne ke sa mutane da dama ke soma nuna ayan tambaya kan yanda abubuwa ke gudana, ganin cewa irin wadanna mahara suna abkawa kauyukan da ake jibge irin wadanna jami'an tsaron ne su kuma yi yanda suke su.

Su kamsu jami'an tsaron basu tsira ba a hannu wadanna maharan,a yanzu dai babu wanni ofishin yan sanda daga babban birnin Maiduguri zuwa Biu ko kuma da Maiduguri zuwa Bama hakama daga Maiduguri zuwa Damaturu.

Haka kuma babu wani kauye babba da zaka ga hada-hadar mutane sakamakon irin wanna hare-haren.

So dayawa Gwamnar jihar Borno Kashim Shattima kan roki masauna wadanna garuruwa da kada su fice daga garuruwasu,dayimasu alkawarin cewa za'a samamasu jami'an tsaro sai daihakan bai canja komai ba.

XS
SM
MD
LG