Accessibility links

Jikin Nelson Mandela Yayi Tsanani


Hoton da aka dauka na Nelson Mandela lokacin bukin tuna ranar cikarsa shekaru 94 da haihuwa, ran 18 Yuli, 2012.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce likitoci sun shaidawa shugaba Jacob Zuma cewa lafiyar madugun yaki da wariya ta kara tabarbarewa daga asabar din nan

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce lafiyar sanannen madugun yaki da wariyar launin fata, Nelson Mandela, ta kara tabarbarewa zuwa hali na "mutu-kwakwai-rai-kwakwai," makonni biyu a bayan da aka kwantar da shi a asibiti ana yi masa jinyar ciwon huhu.

Kakakin shugaban kasar, Mac Maharaj, ya ce likitoci sun fadawa shugaba Jacob Zuma cewa lafiyar Mr. Mandela ta kara tabarbarewa daga ranar asabar zuwa jiya lahadin.

Shugaba Zuma ya samu labarin halin da Mr. Mandela yake ciki ne jiya lahadi da maraice, a lokacin da ya kai ziyara zuwa wani asibitin Pretoria inda aka kwantar da tsohon shugaban ana yi masa jinya. Mukaddashin shugaban jam'iyyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya rufa ma shugaba Zuma baya zuwa asibitin.

Maharaj ya fadawa VOA cewa Mr. Zuma yana son tabbatarwa da al'umma cewa likitoci su na bakin kokarinsu domin kyautata lafiyar Mr. Mandela. Shugaba Zuma yace ana lura sosai da Madiba, watau sunan Me. Mandela na gargajiya.
XS
SM
MD
LG