Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Ruwan Yakin Amurka Ya Fara Sintiri A Kudancin Tekun China


Jirgin yakin ruwan Amurka ya fara sintiri a yankin ruwan da ke kusa da Scarborough, yankin da kasashen China da Phillippines ke takaddama a kai. wannan dai shi ne karo na biyu a cikin watan da ya gabata.

Sojojin Amurka sun ce daya daga cikin jiragen ruwan yakinsu da ke tekun kudancin Sin ya yi sintiri a yau Litinin a kusa da Scarborough Shoal da ake takaddama akai tsakanin China da Philippines.

USS Preble ya yi tafiyar mil 12 a yankin ruwan ne a wajejen Scarborough, a wani yunkuri na kalubalantar ikrarin da suke yi da kuma tabbatar da hanyar ta kasance a bude, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka nuna, a cewar mai magana da yawun kwamandan jirgin mai suna Seventh Fleet, Clay Doss.

Wannan shi ne karo na biyu da sojojin Amurka suka samu damar ratsawa a yankin cikin watan da ya gabata.

A lokacin da yake magana a wurin wani taron tsaro na kasa-da kasa a Singapore a ranar Laraba, shugaban sojojin ruwan da suke aiki, Admiral John Richardson, ya ce sukan yi rangadin yankin ruwan cikin yanayi na tabbatar da adalci a kuma lokaci-lokaci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG