Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Yi Sauye Sauye A Tsarin Shige Da Ficen Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump yana shirin sanar da tsarinsa na shige da fice a yau alhamis, tsarin da zai rage bada izinin zama Amurka bisa dalilan dangantakar iyali da kuma dalilan jinkai.

A jawabinsa ga manema labarai, wani babban jami’in gwamnatin yace shirin zai bada karfi kan kula da harkokin tsaro da kuma fifiko kan cancanta, da ya jaddada cewa, batu ne da yake karo da wadansu batutuwa da dama.

Bisa ga tsarin na shugaba Trump, za a ci gaba da ba kimanin mutane miliyan daya da dubu dari izinin zama a Amurka kowace shekara, sai dai za a sauya tsarin yadda ake kasawa, inda za a bada fifiko kan kwararru da kuma mutane masu ilimi da za a iya dauka aiki ko kuma zasu iya zuba jari a maimakon wadanda suke da dangi a Amurka, ko kuma bukatun jinkai.

A halin yanzu kashi goma sha daya cikin dari ake ba izinin zama amurka da suke da kwarewa, kashi sittin da shida cikin dari, sabili da suna da dangi dake da izinin zama Amurka.

A karkashin sabon shirin, za a rika ba kashi hamsin da bakwai cikin dari na wadanda suke da kwarewar aiki izinin zama Amurka, yayin da za a warewa wadanda ke da dangi a Amurka kashi talatin da uku cikin dari kawai, wadanda suke da bukatun jinkai kuma kashi goma cikin dari daga kashi ishirin cikin dari da ake badawa a halin yanzu.

Za a soke baki daya tsarin bada izinin zama Amurka ta hanyar tambola a ake kira Visa Lottery, wanda a halin yanzu ake ba mutane dubu hamsin kowacce shekara da suka fito daga kasashen da basu da mutane da yawa a Amurka izinin shigowa da zama kasar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG