Accessibility links

'Yan Najeriya na Cigaba da Bayyana Ra'ayinsu kan Taron Kasa


Shugaban taron kasa

'Yan Najeriya na cigaba da bayyana ra'ayinsu kan taron kasa da ya shiga kwana ta uku yau

Yayin da taron kasa ya shiga kwana ta uku cikin watanni uku da aka diba masa 'yan Najeriya na cigaba da bayyana ra'ayinsu.

Ra'ayin talakawan Najeriya ya rabu biyu gameda taron. Wasu na gani taron nada anfani wajen duba matsalolin kasar a wani gefen kuma wasu na ganin taron tamkar barnar kudi ne kawai.

Malam Abdullahi daga jihar Neja yace taron na da kyau domin korafe-korafe sun yi yawa kan alamurorin dake faruwa a kasar. Wasu da dama suna ganin an dannesu. Yana da kyau a samu filin da za'a samu masalaha. Wanda aka danneshi a bashi hakinsa. Wanda kuma ya danne wasu a ja masa kunne kada ya kara. A kare taron da samun masalaha kyakyawa.

Wani kuma cewa ya yi taron kasar za'a dai yi ne amma bashi da wani anfani. Menene anfanin wakilan da aka zaba? Wato duk kudin da ake kashewa a kan wakilan sun tafi a banza ke nan. Kafa wani taron kasa tamkar cewa aikin da 'yan majalisa ke yi bashi da wani anfani. An zabo wasu mutane wadanda kowanensu zai samu fiye da nera miliyan goma sha. Idan an hada kudin da za'a kashe a kansu ya isa a yiwa talakawa aiki da zai anfanesu.

Abdulhamid El Wazir cewa yayi tun da ana baiwa jihohin da suke da arzikin man fetur wasu kason kudi na musamman to jihohin dake samarda wutar lantarki kamar jihar Neja yakamata su ma a basu wani kaso na musamman. A taron kasa yakamata a tattauna irin wannan batun.

Daya daga cikin wakilan taron daga jihar Neja Barrister Haladu Ibrahim yace zai yi iyakacin kokarinsa wajen gabatar da bukatun al'ummarsa sai dai yace ba zasu tattauna matsalar da ta shafi mata ba. Yace tun lokacin Obasanjo a ka soma tattaunawa kan alamuran da suka shafi mata. A gwamnatin Jonathan ma akwai mata da yawa.

Ga karin bayani

XS
SM
MD
LG