Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joe Biden Na Shirin Gabatar Da Albishir Ga Al’ummar Amurka


Joe Biden

Zababben Shugaban Amurka, Joe Biden, na shirin gabatar da albishir ga al’ummar kasar, da kuma inda kasar zata dosa a ranar Laraba, lokacin rantsar da shi.

Kokarin shi na bude sabon babi, da hada kan kasar, bayan kwashe shekaru 4 na gwamnati Donald Trump mai barin gado, wadda, a cewar wani jigo a gwamnatin ta Biden jiya Lahadi, "ta kawo rarabuwar kawunan ‘yan kasar."

Daraktar yada labarai ta Biden Kate Bedingfield, ta shaidawa gidan talabijin na ABC cewar “Sabon shugaban kasar zai fido da wani jadawali dai zai hada kan ‘yan kasar da kuma ganin anyi aiki tare.”

Ta kuma kara da cewar “Ina ganin wannan shine abun da duk Amurkawa ke bukata, suna bukatar gwamnati da ke da alkibila akan aiwatar da abubuwan da suka dace, da kuma taimaka musu akan al’amuran su na yau da kullum.”

Amurkawa miliyan 81 ne suka zabi Biden, a dalilin tsare-tsare da yake da su na ciyar da kasar gaba, da kuma aiki tare da kowa, a cewar Kate.

Biden a shirye yake a rantsar da shi a gefen majalisar dokokin kasar a ranar 20 ga wannan watan da misalin karfe 12 rana. Bisaga al’ada duk bayan shekaru 4 ana gabatar da wannan bukin, amma a bana za’a gabatar da shine cikin dari-dari saboda abun da ya faru a ranar 6 ga wannan watan.

Biyo bayan abun da magoya bayan Trump suka yi na hargitsa majalisar kasar, wanda shugaban mai barin gado ya umurce su da su yi tattaki zuwa majalisar, don hana tabbatar da sakamakon zaben da wakilan electoral college suka yi na zaban Biden a matsayin sabon shugaban kasar.

Karin bayani akan: Joe Biden, Donald Trump, da Shugaban Amurka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG