Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Kerry Zai Tattauna Da Ministoci A Kenya


Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, yanzu haka yana Nairobi ta kasar Kenya. Inda zai tattauna da ministocin harkokin wajen kasashen Afirka ta Gabas, kana zai yada zango a kasar Sudan ta Kudu domin tattaunawa da mahukuntar kasar domin ganin kasar bata sake afkawa cikin wani yakin basasa ba.

Sai dai kuma Kerry zai tattauna da shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyata, kafin ya gana da ministoci wadanda zasu tattauna yadda za a shawo kan hana sabuwar kasar Sudan ta Kudu afkawa cikin wani sabon rikici.

Mutanen kasar ta Sudan ta Kudu dai, sun jima suna cikin halin 'ka 'ka na kayi. Kamar yadda wani babban jami'in harkokin waje ya shaidawa manema labarai.

Rashin kwanciyar hankali a kasar ta Sudan ta Kudu, ya haifarwa Miliyoyin mutane asarar matsugunnan su, kana aikin jin kai ya zame wani babban alkakai, wanda hatta kasashen duniya ma sun rasa ta yadda zasu bullo wa al’amarin.

Kasar Sudan ta Kudu dai ta jima cikin halin zamar dar-dar ne tun daga lokacin da suka samun yancin su daga kasar Sudan a cikin shekarar 2011.

Tun daga wannan lokacin ne rikici ya barke wanda ya haifarwa kasar yakin basasa.

Haka kuma Kerry, da sauran ministocin harkokin wajen kasashen Afirka ta gabas sun shirya tattaunawa akan kasar Somalia, wadda take hasashen ganin ta gudanar da zaben yan majilisar kasar dama na shugaban kasa wanda hakan na iya kawo musu zaman lafiya.

haka kuma a cikin wannan makon ne Kerry zai ziyarci Najeriya, inda zai tattauna da shugaban kasar wadda ‘yan ta'addar Boko Haram ta kashe sama da mutane dubu 20 tun daga shekarar 2009.

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG