Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kace Nace Tsakanin Donald Trump Da Mahaifin Wani Musulmin Sojan Amurka


Cacar baki tsakanin dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump da mahaifin wani sojan Amurka musulmi da dan kunar bakin wake ya kashe a Iraqi a 2004, shine ya mamaye yakin neman zaben shugabancin Amurka a jiya Litinin.

Ana ci gaba da cacar bakin ne tun ranar Alhamis lokacin da Khan ya bayyana a babban taron jam'iyyar Democrat, inda ya mabci aikin sojan dansa a maazan martanin shirin Trump na takaita musulmi shigowa Amurka.Jawabin nasa shine yafi dauke hankali a taron na kwanaki hudu.


A hira da sashen Urdu na MA jiya Litinin,an tambayi Khan ko da wani amfani da ci gaban wannan cacar bakin, yace kwarai kuwa domin galibin 'yan Republican sun yi kira ga Donald Trump ya daina irin maganganun nan ba kan musulmi kadai ba, amma harda sauran tsiraru.


Khan yace ya damu kan makomar shugabancin Amurka idan aka zabe shi, yana kokonton ko sojojin Amurka zasu mutunta umarnin Trump

XS
SM
MD
LG