Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Jam'iyyar Republican Su Ja Kunnen Dan Takararsu - Inji Khan


Khizr Khan da matarsa

Mahaifin sojan Amurka nan Captain Humayun Khan, yayi kira ga Shugabannin Jamiyyar Republican da su ja kunnen dan takarar shugaban kasar su Donald Trump daya daina anfani da sunan dan sa, wurin kamfe domin da yawan mutane zasu kalli hakan a matsayin kaskantarwa ga dan nasa, wanda ya sadaukar da rayuwar sa wurin gudanar da aikin kasa.

Mahaifin Captain Khan, Khizr Khan yayi wannan kiran ne sailin da yake Magana jiya lahadi a gidan talabijin na kasa yana cewa sam Trump bai dace da zamowa wanda zai shugabanci kasa irin Amurka ba.


Ya bayyana dan takarar na jamiyyar Republican a matsayi mai son kansa da kuma yawan koda kansa domin burgewa, akan haka yayi kira ga ‘Yan jamiyyar irin su Micth McConnell da Paul Ryan da su fito sarari domin su fada wa mutane aibun dan takarar nasu.


Wannan bawan Allah Khan, shida matarsa Ghazala, mahaifiyar Captain Humayan Khan sun fito fili ne, a cikin satin data gabata lokacin da suka bayyana wajen gangamin jamiyyar Democrat inda suka yi bayani game da dan su wanda aka kashe a sakamakon tashin wani Bomb da dan kunar bakin wake ya tayar akasar Iraq, kana kuma nan take suka jaddada goyon bayan su ga ‘yar takarar shugaban kasar jamiyyar Republican Hillary Clinton.


Shi dai Khan dan asalin Pakistan ne da yazo nan Amurka yayi jawabi mai sosa rai ga gangamin taron jamiyyar Democrat yace zaiyi wahala ace shida iyalan sun samu damar zuwa Amurka karkashin irin tsarin da Trump yake neman samarwa a manufofin sa na shige da fice.

XS
SM
MD
LG