Accessibility links

Sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo sun bayyana dukiyoyinsu da kadarorinsu.

Wannan bayyana kadara, ta mutumin dake kama aiki a gwamnatance, na cikin tsarin da kundun kasa ta tanada. Kamar yadda Barrista Mainasara Kogo Ibrahim yayi bayani.

“Tsarin mulki sashe na biyar na tsarin mulki sakin sashe na biyu ya bada damar cewa ofisoshi ko jami’an gwamnatoci wadanda wajibi ne, kafin su rike mukamin nan, dole ne suyi bayanin abubuwan da suka mallaka. Wadannan abubuwa sun kama tun daga ma’aikaci tun daga mataki na biyar, har zuwa mukamin shugaban kasa” a cewar Barrista Ibrahim.

Wani batu da ya dauki hankali shine yadda shugaba Buhari da mataimakinsa suka bayyana kadarorin nasu, ganin cewa a rubuce suka bada shi ga hukumar dake kula da wannan fanni. Yanzu kungiyoyi masu zaman kansu sun fara korafi.

Dr. Jirbin Ibrahim, na cibiyar habbaka demokradiyya yayi tsokaci.

“Ba shakka ya dame mu. Ni kaina nayi rubuce-rubuce da yawa, da shugaba Jonathan yaki bayyana wa”.

Ko wani hukunci kundun tsarin mulkin Najeriya ya tanadarwa wadanda suka sabawa doka? Barrista Ibrahim yayi karin haske.

“Akwai hukunci daban-daban da doka ta bada dama. Za’a iya sauke mutum daga kujerar da yake rike da ita”.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa sun bada izini ga dukkan wani dan kasa da yake so ya san kaddarorin nasu, da yaje hukumar da aka dorawa alhakin kula da sanin kaddarorin ma’aikatan gwamnati ko “Code of Conduct Bureau” a turance.

XS
SM
MD
LG