Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaduna: An Rufe Kasuwannin Da Ke Kusa Da Makarantar Sojoji Ta NDA Bayan Harin ‘Yan bindiga


Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai (Facebook/El Rufai)
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai (Facebook/El Rufai)

“Gwamnatin jihar Kaduna ta ba da umarnin rufe kasuwannin na sati-sati na garin Ifira da kuma garin Sabon Birnin Daji.” In ji Samuel Aruwan.

Sa'o'i kadan da tabbatar da kashe mutum biyu da kuma sace mutum daya a makarantar horon aikin sojan Najeriya da ke Kaduna, gwamnatin jihar ta sanar da rufe wasu kasuwanni da ke makwabtaka da makarantar da aka kai wannan hari.

Harin 'yan-bindigan dai ya baiwa mutane da yawa mamaki ganin yadda ake kallon makarantar horar da sojojin a matsayin madogarar tsaron 'yan kasa da kuma kusanchin ta da wasu cibiyoyin tsaro.

Sai dai gwamnatin jihar ta Kaduna ta ce tuni jami'an tsaro su ka dauki matakan da su ka kamata, in ji kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan.

“Wannan abu da ya same mu, abu ne wanda ba mu ji dadi ba, ita hukumar makarantar da kanta ta yi bayani cewa, akwai jami’ai biyu da muka rasa da kuma jami’i daya wanda aka yi garkuwa da shi.” In ji Aruwan.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar Kaduna na daukan matakan da ya kamata domin ganin an shawo kan matsalar ta tsaro.

“Gwamnatin jihar Kaduna ta ba da umarnin rufe kasuwannin na sati-sati na garin Ifira da kuma garin Sabon Birnin Daji.” In ji Aruwan.

To ko me wannan harin'yan-bindiga ke nunawa a kokarin yaki da matsalar tsaro? Dr. Yahuza Ahmed Getso, na cikin masu fashin baki akan harkokin tsaro a Najeriya.

“Wannan yana nuna gazawa da rashin kulawa da kuma rashin hadaka a tsakanin hukumomin tsaro, domini dan ka dubi inda aka kai wannan hari da hukumomin sojojin kasa da na sama da babban ofishin GOC,” babu nisa a cewar Dr. Getso.

Dama dai gwiwowin wasu'yan Kasa sun riga sun yi sanya game da yaki da 'yan-bindiga a Najeriya saboda yadda jami'an gwamnati da dama ke nuna bukatar mutane su fara kare kawunan su. Manjo Yahaya Shinko mai ritaya na ganin akwai abubuwan dubawa game da wannan batu.

“Kamar ta maganar gwamnan Katsina ne, Jama’a yakama ta su rika tanadin abun da za su kare kansu da kansu. In kana sa ran gwamnati za ta maka wani abu ga abin da yake faruwa da ita.”

Hare-haren 'yan-bindiga a jihar Kaduna dai ya mamaye wasu yankunan Kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chukun, Igabi da Zangon Kataf, sai dai kuma wannan ne karon farko da 'yan-bindigan su ka shiga makarantar da a nan ne ake horar da jami'an tsaro don kare Kasa.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00


XS
SM
MD
LG