Accessibility links

kwanakin kadan a yi zaben shugabannin majalisar dattawa da na wakilai, jam'iyyar APC mai mulki ta zabi Femi Gbajabiamila a matsayin dan takarar ta a neman shugabancin kakakin majalisar wakilai.

Jami’iyar APC mai mulki ta tsayar da Femi Gbajambiamila daga jahar Legas a matsayin dankararta a neman kujerar kakakin Majalisar Wakilai.

Femi ya samu nasara ne akan abokin hamayyarsa, Yakubu Dogara daga jahar Bauchi wanda ya samu kuri’u uku yayin da shi Femin ya samu kuri’u 154.

Sakataren APC, Mai Mala Boni ne ya ayyana Femi a mastayin dan takarar bayan kammala jefa kuri’a yayin da ake tunkarar zaben a mako mai kamawa.

“A yanzu zan jagorance ku ne a matsayi na Kakakin majalisa ba kamar a tsohon mukamin shugaban ‘yan adawa ba.” Inji Femi.

Wasu daga mukarraban Dogara da shi kansa, wato su kimanin 20 sun fice daga dakin taron a fusace bayan da aka kammala zaben.

Dan majalisa Ahmad Baba Kaita ya ce sun yiwa jam’iyya biyayya ne wajen zaben Gbajambiamila.

“Babbar matsala itace idan kowa ya ce zai fito ya ce a bashi wannan mukami, idan ba a bashi ba ya ce zai tafi, ina jam’iyyar APC za ta je?.” Inji Kaita.

Shi kuwa M.T. Manguno shi aka tsayar a matsayin mataimakin kakakin majlisar, ya kuma ce sakamakon wannan zabe ya nuna cewa kan ‘yan jam’iyyar a hade ya ke.

“Wannan zabe da aka yi na APC ya nuna a fili cewa mambobin wannan jam’iyya suna san wannan tafiyar, saboda haka wadanda ba sa tare da mu za mu same su mu ce musu su zo a yi wannan tafiya har ma da na PDP” Inji Manguno.

Ga karin bayani a rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:

XS
SM
MD
LG