Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalaman Melania Trump Sun Ba Mutane Mamaki


Melania Trump
Melania Trump

Kalaman uwargidar shugaban Amurka na daren jiya Talata yayin babban taron jam'iyyar Republican sun sha bamban da na mijinta, Shugaba Donald Trump, lamarin da ke ta ba masu nazari mamaki.

Uwargidar shugaban Amurka Melania Trump, ta bayyana cewa ta tausaya wa dubun dubatan Amurkawa da suka harbu da cutar coronavirus, inda ta sha bamban da mijinta, wanda bai cika jaddada tsanancin cutar ba.

Uwargida Melania, ta fada a jawabin da ta yi da maraice a ciki lambun shakatawa na Rose Garden da ke Fadar White House cewa, “Ina matukar tausaya wa duk wadanda suka rasa wani dan uwansu. Ina addu'a ga duk wadanda ba su da lafiya ko su ke cikin wahala."

"Na san mutane da yawa suna cikin damuwa da kuma rashin mafita," in ji ta. Ta kara da cewa, "Ina son ku san cewa ana tare da ku."

Kalaman nata sun yi matukar bambanta da na dare biyu da su ka gabata masu cike da caccaka irin na siyasa, inda magoya bayan Trump suka yi ta sukar abokin hamayyarsa na Democrat, Joe Biden yayin da a gefe guda kuma suka yi ta yabon Trump kan irin matakan da ya dauka kan cutarcoronavirus da kuma illar da ta yi ma tattalin arzikin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG