Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kama Al-Bashir: Afirka sun yi kuskure


Shugaban Sudan, Omar Al-Bashir
Shugaban Sudan, Omar Al-Bashir

Kamar yadda aka sha barazanar danko Shugaban Sudan Omar Al-Bashir, yanzu haka ma an bada dokar cafko shi daga wajen taron da ake yi a Afrika ta Kudu na kungiyar kasashen Afirka.

Farfesa Sani Fagge mafashin bakin difilomasiyya yana ganin tun farko kasashen Afirka sun yi kuskuren sa hannu amincewa da kotun duniya. Mai fashin baki kan al’amuran siyasa Farfesa Kamilu Sani Fagge yace sauran Turawan yamma ba su sakawa irin wannan yarjejeniya hannu ba.

Wannan ce ta sa duk tsiyar da suka shuga ba sa fuskantar wannan barazana. Ya kara da cewa hatta yarda da Al-Bashir din yayi na raba Sudan ta Kudu da ta Arewa yayi ne don ganin cewa zai sami sassauci daga kotun ta duniya.

YA kara da cewa karfin tattalin arziki da kuma juya kambin siyasar duniya ya dadawa Turawan na yamma karfi wajen yadda kasashen Afirka ke neman tallafi daga wajensu. Ya bada misalin da Amurka da Isra’ila game da siyasar duniya amma ba a musu wani abu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG