Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru: Hukumomi Sun Ja Daga Da 'Yan Jarida


'Yan sanda kwantar da tarzoma a Kamaru
'Yan sanda kwantar da tarzoma a Kamaru

Kungiyar ‘yan jaridar kasar Kamaru ta yi kira ga hukumomi da su gaggauta sako ‘yan jarida ba tare da wasu sharuda ba, wadanda aka kama yayin da suke daukar rahoto a wurin zanga-zangar kin jinin gwamnati a wannan mako.

‘Yan sanda sun tsare akalla ‘yan jarida takwas a yayin da suke aikin daukar rahoto a wurin zanga-zanga a ranar Talata kana suka binciki gidajen wasu ‘yan jarida hudu, aka kuma kwace ko lalata musu na’urorin aiki.

Ya zuwa yanzu akwai akalla dan jarida guda da ke kulle.

Shugaban kungiyar ‘yan jarida da ke yankin masu magana da turancin Ingilishi a Kamaru, Jude Viban, ya ce an kama wani dan jarida Tah Javis Mai tare da wasu manema labarai bakwai a babban birnin kasar Yaounde da Douala.

Viban, ya ce yana Allah wadai da babbar murya a kan tsare ‘yan jaridar ba bisa doka ba a Kamaru.

Ya ce bai kamata ana daukar ‘yan jarida tamkar masu aikata laifi ba, saboda kawai suna gudanar da aikin su.

"Muna Allah wadai da kamen abokan aikin mu da suka je daukar rahoto amma ba wai taya masu zanga-zanga ba, kana aka kwashe su aka kuma kulle su a wasu wurare da ba’a bayyana ba, haka kuma aka hana su ganin lauyoyinsu da ma abokan aikin su," in ji Viban.

Shugaban na kungiyar 'yan jarida ya ci gaba da cewa "wannan damuwa ce ga dimokaradiyar mu kuma abin takaici ne da yake ci gaba da faruwa. ‘Yan jarida na cikin mawuyacin lokaci a Kamaru."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG