Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Sun Kashe Akalla Mutane 16 A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Kamaru


Wasu da ake kyautata zato mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kashe akalla mutum 16 tare da jikkata wasu 7 a jiya Lahadi a wani hari na gurneti da aka kai a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewacin Kamaru, a cewar Jami’an kasar.

Maharan sun jefa gurnetin ne akan wasu mutane da ke barci a cikin sansanin a kauyen Nguetchewe, kamar yadda magajin garin yankin Medjeweh Boukar ya fada wa kamfanin dillanci labaran Reuters. Akwai mutane kusan 800 a sansanin a cewar Boubakar.

Kauyen Nguetchewe dai na kusa da iyakar Najeriya da kasar.

Mazauna yankin sun fada wa Boukar cewa mutum 16 suka mutu. A baya wani jami’in tsaro ya ce mutum 15 ne suka mutu. An kuma kai wadanda suka jikkata a wani asibiti da ke kusa, a cewar su.

Facebook Forum

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG