Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Ta Lashe Matsayi Na Uku A Gasar AFCON


'Yan wasan Kamaru bayan da suka lashe matsayi na uku a gasar AFCON bayan doke Burkina Faso
'Yan wasan Kamaru bayan da suka lashe matsayi na uku a gasar AFCON bayan doke Burkina Faso

Wani abin mamaki a wasan shi ne Burkina Faso ce ta fara zura kwallaye uku a ragar Kamaru cikin mintina 49. 

Kasar Kamaru da ke karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta lashe matsayi na uku a gasar cin ta AFCON.

‘Yan wasan Indomitable Lions sun lallasa takwarorinsu na Burkina Faso da ci 5-3 a bugun fenariti bayan da aka tashi da ci 3-3.

Wani abin mamaki a wasan shi ne Burkina Faso ce ta fara zura kwallaye uku a ragar Kamaru cikin mintina 49.

Amma bayan kukan kura da ta yi, Kamaru, ta farke dukka kwallaye ukun, lamarin da ya kai wasan ga bugun fenariti bayan da aka tashi da ci 3-3.

Kamaru dai ta kare a wasan neman matsayi na uku ne bayan da ta sha kaye a hannun Egypt bayan bugun fenariti.

Hakan ya ba Egypt din damar zuwa wasan karshe tare da Senegal.

Ita kuma Senegal ta kai wasan karshe ne bayan da ta doke ‘yan wasan Burkina Faso da ci 3-1.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG