Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Kare Bayanan Sirri a Shafukan Sada Zumunta Ta Fara Aiki a Turai


Badakalar bayanan sirri ta Facebook
Badakalar bayanan sirri ta Facebook

Kasashen kungiyar tarayyar turai sun samar da wata doka wacce za ta kare bayanan sirrin al'umar yankin tun bayan da aka samu kamfanin shafin sada zumunta na Facebook da yin sakaci da bayanan sirrin masu amfani da shafin.

Wata sabuwar doka da aka fitar a nahiyar turai kan yadda za a rika kiyaye bayanan sirrin jama’a tare da yadda kamfanoni za su yi garambawul kan tsarin da suke bi wajen karbar bayanan da sarrafa su, ta fara aiki a jiya Juma’a.

Wannan doka ta fara aiki ne bayan da aka yi ca akan kamfanin shafin sada zumunta na Facebook a Amurka, kan wata badakalar amfani da bayanan sirrin jama’a.

A karkashin dokar, wacce hukumar kula da bayanan jama’a da kare su da ake kira GDPR a takaice ta samar, kamfanoni za su ci gaba da karban bayanan sirrin masu mu’amulla da su daga wayoyinsu da manhajoji da kuma shafukansu.

Amma za su rika fadawa mutane dalilin karbar bayanan da kuma amfani da za su yi da su.

Wannan doka, za ta shafi daukacin kasashe 28 da ke cikin kungiyar tarayyar turai, amma kuma za ta shafi har da wasu manya da kananan kamfanonin Amurka da ke nahiyar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG