Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Jiragen Ruwa Na Maersk Zai Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 600 A Najeriya


Kamfanin Maersk
Kamfanin Maersk

Najeriya ta samu jarin dalar Amurka miliyan 600 na samar da kayayyakin aiki a tashar jiragen ruwa daga kamfanin jigilar kayayyaki na kasar Denmark A.P. Moller-Maersk MAERSKb.CO, kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar ranar Lahadi.

WASHINGTON, D. C. - An samu nasarar shirin zuba jarin ne a wata ganawa tsakanin shugaba Bola Tinubu da shugaban Moller-Maersk Robert Maersk Uggla a gefen taron tattalin arzikin duniya da aka gudanar a kasar Saudiyya.

"Mun amince da Najeriya, kuma za mu zuba jarin dala miliyan 600 a kan kayayyakin da ake da su, sannan za mu sanya tashoshin jiragen ruwa su zama masu daukar manyan jiragen ruwa," in ji Uggla a yayin taron

Najeriya ta yi alkawarin gyara tashoshin jiragen ruwanta, ciki har da ta birnin Legas, babban birnin kasuwancin kasar, domin rage cunkoso da ke kawo cikas ga harkokin kasuwanci.

A yayin taron, Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tallafa da inganta tashoshin jiragen ruwanta don bunkasa harkokin kasuwanci, da rage cin hanci da rashawa da kuma inganta ayyuka yadda ya kamata.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG