Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Microsoft Ya Dauki Aniyar Yalwata Kasashen Afrika


Microsoft
Microsoft

Wata sanarwar da kamfanin Microsoft ya fitar na cewa zai bude sababbin rassa 2 a kasashen Afrika, hakan na nuna alamar cewa kamfanin ya daura damarar girka kansa a cikin nahiyar.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne dai kamfanin ya bude wadannan rassan guda biyu, daya a birnin Lagos kana dayan kuwa a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Shugabar reshen Microsoft a nahiyar Afrika, Amrote Abdella, tace bude rassann na nuna cewa yazo da niyyar zama mai dadewa a nahiyar.

Kamfanin kimiyyar da fasahar dai ya kai shekaru 25 yana aiki a kasashen Afrika, kuma a cikin watan Maris ne ya kara bude wasu cibiyoyi 2 a kasar Afrika ta Kudu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG