Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Pfizer Ya Yi Kokarin Bata Sunan Atoni-Janar A Najeriya


Kamfanin Pfizer Ya Yi Kokarin Bata Sunan Atoni-Janar A Najeriya

Takardun sirri na diflomasiyya daga ofishin jakadancin Amurka a Najeriya sun nuna cewa kamfanin harhada magungunan ya nemi bata sunan atoni-janar domin a janye karar kamfanin da Jihar Kano ta shigar.

Dandalin kungiyar nan ta 'yan fallasa da ake kira "Wikileaks" ya buga wasu takardun diflomasiyya na sirri daga ofishin jakadancin Amurka a Najeriya dake cewa kamfanin harhada magunguna na Pfizer ya yi hayar wasu masu bincike domin su samo masa bayanan batunci na zarmiya da cin hanci a kan wani atoni-janar a kasar.

Kamfanin yayi hakan ne da niyyar matsawa Najeriya lamba a kan ta janye karar kamfanin da ta shigar dangane da gwajin wani maganin sankarau a kan yara kanana.

Jihar Kano, ita ce ta shigar da karar kamfanin na Pfizer a saboda ta ce yara da yawa sun mutu a lokacin da ake gwajin maganin kashe kwayoyin cuta mai suna "Trovan" a kan su.

Daga baya a wannan shekarar, Jihar ta Kano ta daidaita da kamfanin Pfizer a kan diyyar dala miliyan 75.

Jaridar Guardian ta Britaniya ta ce wadannan takardun diflomasiyya da "Wikileaks" ta fallasa su na magana ne kan ganawar da aka yi a tsakanin wani manaja na kamfanin Pfizer da jami'an Amurka. Takardun sun ambaci jami'an Amurka su na fadin cewa masu binciken da kamfanin Pfizer yayi hayarsu, su na mika bayanan batuncin da suka tono kan wannan atoni-janar ga jaridu na Najeriya domin matsa masa lamba a kan ya janye wannan kara.

XS
SM
MD
LG