Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Hudu Suna Hanu Kan Zargin Satar Na'rorin Rigistar Mazu Zabe A Tashar Jiragen Sama Dake Legas


Murtala Muhammed International Airport in Lagos, Nigeria (File Photo)
Murtala Muhammed International Airport in Lagos, Nigeria (File Photo)

Rundunar 'Yansandan Najeriya Tace ta tsare mutane hudu kan zargin suna da hanu a satar na'urorin rigistar masu zabe guda ashirin,bayan an sauke su a tashar jiragen sama a Legas ranar litinin.Jumma'a ce aka kama mutanen. Ana kan bincike ko da hanun wadansu a satar

Rundunar ‘Yansandan Najeriya ta ce ta tsare mutane hudu kan zargin satar na’urorin aikin zabe a tashar jiragen sama kasr dake Legas. A daren jiya jumma’a ce rundunar ta bada labarin kama mutanen.

Ana zargin sun saci na’urorin registar masu zabe ashirin,bayan an sauke kayan a tashar jiragen ranar litinin. Hukumomi suka ce an gano 16 daga cikin na’urorin.‘Yansanda suna bincike ko akwai hanun wadansu a satar na’uorirn.

Jami’ai suka ce satar na’urorin ba zai yi tasiri ba a shirin rigistar masu zabe da aka ayyana farawa ranar 15 ga watan janairu,shirin zai dauki mako biyu.

Ahalin yanzu kuma ‘Yansanda a Kenya sun kama ‘yan kasar Singapore biyu a tashar jiragen sama dake Nairobi kan zargin suna kokarin safarar hauren Giwaye da nauyinsu ya kai kilo 92.

Hukumar kula da gandun dajin kasar tace wasu karnuna da aka horas kan wan nan aiki ne suka gano hauren da aka saka cikin jakakkuna hudu,dab da ana shirin lodi cikin wani jirgi da zai tashi zuwa Thailand a daren jiya jumma’a.

XS
SM
MD
LG