Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Sarrafa Tumatur Erisco Na Barazanar Rufe Kamfanin


Rashin samun kudaden Dalar Amurka domin sayo kayan gudanar da aiki ya tilastawa wani kanfanin sarrafa Tumatir rufe kamfanin, abin da kuma zai jefa dubban ma'aikata cikin halin rashin aiki a Najeriya.

Dubban ma’aikatan kamfanin sarrafa Tumatirin gwamgwani da ake kira Erisco, sunyi zanga zangar adawa da matakin da kamfanin ke shirin dauka na sallamarsu daga aiki. A wani taron manema labarai da shugaban kamfanin ya kira a birnin Lagos, yace daukar matakin rufe kamfanin ya biyo bayan rashin samun kudin Dalar Amurka daga babban bankin Najeriya, domin sayo kayan sarrafa Tumaturin daga kasashen waje.

Haka kuma shugaban kamfanin ya zargi babban bankin Najeriya da baiwa wasu damar shigowa da Tumaturin da aka riga aka sarrafa daga wasu kasashen ketare zuwa Najeriya, lamarin da ke kashe kamfanonin cikin gida.

Bincike ya nuna cewa Dubban matasa ne ke aiki a wannan kamfani kama daga Lagos zuwa wasu jihohin Arewacin Najeriya, musamman ma manoma dake sayarwa da kamfanin Tumaturin da suke nomawa duk lamarin zai shafe su.

Babbar illar ruke kamfanoni ko masana’antu a kasa shine rasa aiki ga dinbin ma’aikata, haka kuma gwamnati zata yi asarar haraji. Yanzu dai abin jira a gani shine ko kukan da kamfanonin cikin gida ke yi zai yi tasiri.

Saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin daga Lagos.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

XS
SM
MD
LG