Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Starbucks Mai Sayar Da Kofi Zai Horas Da Ma'aikatansa Akan Illar Nuna Wariyar Fata


amfanin Starbucks

Cin mutuncin da aka yiwa wasu bakaken fata biyu a wani shagon Starbucks a jihar Philadephia ya sa kamfanin daukar matakin rufe shagunansa dubu takwas dake Amurka domin horas da ma'aikatansa akan illar nuna wariyar fata tare da dabarun yakar nuna wariya

A wani mataki na dakile sukar da ta biyo bayan kama wasu bakaken fata biyu a daya daga cikin shagunansa a kwanakin baya, kantin sayar da shayin gahawa ko kofi na Starbucks, zai rufe shagunansa dubu takwas a Amurka a yau Talata.

Kamfanin ya dauki wannan mataki ne domin ya yi amfani da damar, ya horar da ma’aikatansa dabarun yaki da nuna wariya.

A ranar 12 ga watan Afrilu, wasu bakaken fata biyu a birnin Philadelphia suka shiga shagon na Starbucks, kuma ba su sayi komai, daya daga cikin ma’aikatan kantin ya kira ‘yan sanda, lamarin da ya kai ga aka kama bakaken fatar, matakin da ya janyo zanga-zanga da zargin nuna wariyar launin fata.

Bidiyon wannan sa-in-sa da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ya zamo babban abin kunya ga kantin na Starbucks.

Jim kadan bayan hakan, kamfanin sayar da shayin na gahwa, ya yi maza-maza ya fitar da wani tsari da ya ba kowa da kowa damar shiga shagon ya zauna ko ya yi amfani da bandakinsu, ko da mutum ba zai sayi komai ba.

A baya, manajojin kantunan ne ka yanke shawarar ko za a bar mutane su yi Amfani da bandakin shagunan na Starbucks, idan ba za sayi komai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG