Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin Amurka Zasu Dauki matakai Kan Dumamar Yanayi


Shugaban Amurka Barack Obama Dec. 1, 2015.

A yau Talata ne fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta fitar da sanarwa cewa, taron kolin da ake a birnin Paris, kamfanonin Amurka 73 sun sha alwashin nuna goyon baya ga matakan da aka dauka kan dumamar yanayi.

Cikin manufofin taron a kwai rage iska mai gurbata muhalli da kashi 50 cikin dari da rage amfani da ruwa da kashi 80 cikin dari da sayen makamashin da ake sake sarrafashi ayi amfani dashi.

A yau Talata ne shugaban kasar Faransa, Fransuwa Oland ya sanar da cewa Faransa zata baiwa kasashe Afirka dala biliyan 2 da milayan 100 cikin shekaru hudu masu zuwa, domin samar da hanyoyin makamashin da ake sake sarrafawa da sabunta wadanda ake dasu.

A taron kolin ne yau Talata shugaban Amurka Barack Obama ya gana da kungiyar kasashen da suke kananan tsuburai, da dumamar yanayi ta tayiwa illa.

Yawancin shugabannin kasashen da suka halarci taron kolin jiya Litinin sun amince da ‘daukar matakin kare gandun daji.

XS
SM
MD
LG