Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamun Ludayin Buhari Cikin Shekara Guda


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a lokacin taron kungiyar ECOWAS

A ranar mai kamar ta yau, wato 29 ga watan Mayun shekarar 2015, aka rantsar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a karkashin jam’iyar APC, bayan da ya doke abokin hamayyarsa Goodluck Jonathan na jam’iyar PDP.

Jam’iyar ta PDP dai ta kwashe shekaru 16 tana mulkin Najeriya, sai a wannan lokaci ne kuma mulkin ya bar hannunta.

Mutane da dama, sun kosa gwamnatin ta Buhari ta samar da canji, saboda zargin da ake na cewa gwamnatocin baya sun kassara kasar, musamman ganin yadda cin hancida rashawa ya yi katutu a ko’ina.

Yayin da wasu ke yaba irin kamun ludayin Buhari, wanda ya taba mulkar kasar a baya, wasu kuma suna nuna gazawarsa, inda sukan yi nuni da irin wahalar mai da ake fama da shi da rashin wutar lantarki da tsadar abinci da kuma uwa ba karin kudin man da aka yi.

Gwamnatijn ta Buhari ta kara kudin man ne bayan janye tallafin da ta ke bayarwa a fannin na mai.

Wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa daga Abuja, ya mana dubi kan wasu muhimman batutuwa kan gwamnatin ta Buhari wacce ta cika shekara guda a yau:

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:34 0:00

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG