Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kananan Jam'iyyu Na Taka Rawa a Zaben Turai


Kananan jami’iyyu a Turai suna samun karin goyon baya a zaben gama gari na Majalisar Dokokin nahiyar Turan, zaben da ‘yan siyasa da masu sharhi ke ganin ka iya zama mafi muhimmanci tun shekarar 1979, lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai ta fara gudanar da zaben ‘yan Majalisar nahiyar.

Sakamakon farko da suka fara bayyana a zaben jiya Lahadi na Majalisar mai kujeru 751, zai fuskanci rarraba fiye da lokutan baya. Kananan jami’iyyu da suka hada da masu ra’ayi da kuma masu sukar Kungiyar Taryayyar Turai, suna taka rawar gani sama da mayan jami’iyyu masu matsakaitan ra’ayi da masu tsaurin ra’ayi.

Masu ra’ayin Tarayyar Turan da masu adawa sune zasu raba karfi a sabuwar Majalisar, wacce zata yi aiki tsawon shekaru biyar. Philippe Lamberts shine shugaban jami’iyar masu sukar Tarayyar Turai, ya ce samun rinjayi a sabuwar Majalisar, wani al’amari ne mai muhimmnacin ga jami’iyarsa ta masu ra’ayin rikau.

Da alamar tashin sababbin jami’iyyun ya kashe tasirin da jami’iyar masu matsakacin ra’ayi ta European People’s Party da ta masu ra’ayin ‘yan mazan jiya ta Progressive Alliance of Socialist and Democracy suka dade suna morewa a majalisar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG