Wadannan kananan makamai dake hannun jama’a suna kara hura wutar rikici manoma da makiyaya da ya mamaye jihohin Arewacin kasar da ma wasu sassan kudancin Najeriyar. Rashin dakile wannan al’amari zai iya kaiwa ga sauran iyakokin kasashen Afrika ta Yamma.
Dalilin haka ne ministan harkokin cikin gida na Najeriya Abdurrahman Bello Dambazau ya yi kira ga Jami'an Kasashen ECOWAS da su taimako akan batun tsaro da a halin yanzu ya dauki hankalin mahukuntan Najeriya. Kan haka ne yanzu aka nada Komitin da zai yi aikin samo hanya dakile rikice rikicen.
Kwamishinan ECOWAS mai kula da kasuwanci, zirga zirga mutane da dukiyoyi Alhaji Lawali Shuaibu, ya bayyanawa wakiliyar Muryar Amurkas, Medina Dauda, muhimmancin wannan ganawar.
Ga dai rahoton na Medina a kan taron:
Facebook Forum