Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kannywood Ta Yi Taron Addu'o'i Ga Jaruman Da Suka Rasu

Jaruman Kannywood (Facebook/ Fina Finan Hausa Ahfip/ Khalid Musa, Shehu S. Bello)
Jaruman Kannywood (Facebook/ Fina Finan Hausa Ahfip/ Khalid Musa, Shehu S. Bello)

A bara kadai, masana’antar ta rasa jarumai irinsu, Sani Garba S.K, Zainab Musa Booth (mahaifiyar Maryam Booth,) Ahmad Tage, Isyaku Forest da sauransu.

'Yan masa'antar shirya fina-finai ta Kannywood sun gudanar da taron addu'oi ga abokan aikinsu da suka rasu.

Taron wanda Gidauniyar Kannywood, wato Kannywood Foundation ta shirya, ya gudana ne a Cibiyar Matasa da ke unguwar Gyadi-gyadi a birnin Kanon Najeriya.

Jaruman masana’antar ta Kannywood da wasu masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai da dama sun rasu musamman a shekarar da ta gabata.

Wannan taro ya samu halartar masu rike da mukami a gwamnati, da masu ruwa da tsaki na masana'antar, da masu fada a ji, da tsaffi da kuma sabbin jarumai na masana'antar mata da maza, da kuma sauran jama'ar gari," a cewar shafin Fina Finan Hausa Ahfip.

Jaruman Kannywood a wajen taron addu'o'i (Faceboo/ Fina Finan Hausa Ahfip /Khalid Musa, Shehu S. Bello
Jaruman Kannywood a wajen taron addu'o'i (Faceboo/ Fina Finan Hausa Ahfip /Khalid Musa, Shehu S. Bello

A bara kadai, masana’antar ta rasa jarumai irinsu, Sani Garba S.K, Zainab Musa Booth (mahaifiyar Maryam Booth,) Ahmad Tage, Isyaku Forest da sauransu.

Daga cikin manyan masana’antar ta Kannywood da suka halarci taron addu’o’in, akwai Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Isma’ila Afakalla, Ibrahim Mandawari, Falalu Dorayi, Ado Ahmad Gidan Dabino, Kabiru Mai Kaba da sauran su.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG